Salim smart on the beat Bazan miki karya don ki soni cikin gagawa ba Idan ma nai karyan furenta bazai mini 'ya'ya ba Koda za'ai suka kune na bazan toshe ba Inma na toshe kalmominki bazan ki jiyowa ba Kiban aron lokaci muyo hira Ki gane yanda sonki yai mamaya Na zautu na kamu ki tausaya Na soki ki soni nai magiya ♪ A kallon farko kika sace zuciya Kauna tai zurfi ta kulle idaniya In kika yai watsi dani to zana sha wuya Soyayya ta babu kalarta a duniya Kaunarki zanyi wa tatali Zan nuna so gunki na asali Gareki zan zama adali Zan baki lura da kariya ♪ Zaki na kalaminka ya kauda mini shaku na Nasaba da kamalanka suke kawata kallon na Kasakani a gefenka a ta dama ka dan rike hanu na Muje in nuna ka siriki gun umma da abba na A Sanya mana rana muyo aure Abaka ni ta zaure ka ketare Nai maka hidima rana ko dare Biyayar aure zanyi da tareraya Baiwar Allah ina son ki A soyayya kece zabi na Bawan Allah ina son ka Ni soyayya ka zam zabi na