Sarautar mata sannu Ke che fitila ta gida na Al kyabar mata kyakkyawa Mai kawata kallo na Sarautar mata ce ni Al kyabar mata sannan yar gata gun ango na ♪ Daga ke na kulle kofa bazanchen nai maki kari Wani gatan soyayya zanyi bidda tunda gaki a fari Kin sakankanta ni da kulla da salon so tari tari Yanzu nafara soyayya Yanzu na san da soyayya Yanzu nasamu kariya A tattara yan mata da yawa nasan basu kai ki ba ♪ Samar da irin ka akwai wahala cikin sa maza kai nesa Ga ta yanda kake mini adalchi Hakan ya saka ni a kunyar ka Ni kagama nunan soyayya tunda nazam to matar ka Hakika kai dan sarki ne Miji na mai mulki na ne Bai san yaga baccin rai na ne Mun cin ribar tarayya a so ba a fimu da komai ba ♪ Na barmaka kaina Ta yadda kaso kai ne da guri Uban ya'ya na a guri na ka zarche gatari Zan soya maka suna In kira ka damu sarkin hakuri Taho ango na Ka nunan kauna Ka sanyaya rai na Aljanna nake nema a kasan ka bazan ki biyayya ba ♪ Ina sanka irin san da banyi wa kowa ba Ina jin ka a jikina ban maka karya ba Ni in na rasa ka kasan bazan iya komai ba Duba san ka ya nashe ni Zaman mu yana birge ni Inuwar so ka saya ni A sashi na kaine farko ba a fika mukami ba ♪ Sarautar mata fada mini mi kika so inyi maki take Kin chanchanta in baki mukulin mota kin wuce keke Da ranki ya bace Eh gara a ce in koma tallar panke A kanki na gane cewa soyayya da akwai dadi