Auta Waziri kuke ji malam Prince Production Beat on the miracle Kedai nace miki barni dasu, komai zasu fada Shidai maiko wannan tabbas an samu a gyada In har nasara zakayi makiyi kushe zaya fada Lallai hassada babban ciwo gun mai yi anka fada Nasan koba yau ba, wataran zasu yi haka yan nema (Kwarai) Indai kan sone na shirya na, na dau alkalami Mai kawo kushe ko suka, nan gun ba hurumi Komai sanyi na ruwan randa zafi zai sa shi gumi Haske shine ke haska duhu, wannan sai ilimi Indai har ban mutu ba, nasan basa iya min komai (Basa iya ma komai) Mun saba zama da mutane ne bamu san zasu yi haka ba Kullum a bukatar tasu suke, ko kaine a gaba Indai sun samu kai ka rasa, su bai cin masu ba Nai riban tasu suke hange, koda kai bai maka ba Shidai fanni na rabo, Allah shi ne yaka ba kowa ♪ (Wane mutum) (Wane mutum) ♪ Zanso in fada miki sirrin so, ammah sai da kula Lallai a cikin sa akan dara, har ma ai kwalla Kayan daya cika da inganci ba ayi mai talla Shi so baya son mai wauta, sai an bada kula Naso ki cikin raina, nasan bazan yi kamar ke ba ♪ Halin ki yasa sauran mata suke dada kishin ki Kin dau daraja kima, sannan kin kare mutunchun ki Dawisu adon ki yasa kowa ya ke dada shaukin ki Zan so maganar mu a daidaita, ki fadawa umman ki Na duba kaf a gari, kece dai banga kamar ke ba (Dawisu uwar ado) Komai nisan tafiya wataran za a cimma gari Zan so ku fadawa fatake damo shine sarkin hakuri Hannu daya bai daukan jinka, sai an tara gari Na shida zuma mai kyau ba a sa mai sukari Indai da uwar gayya, ba a damu daku yan daidai ba (Wane mutum) (Wane mutum) Inda uwar gayya, ba a maganar saura Ehh inji Auta Waziri malam