Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Dan Majen Gombe lyrics

Artist: Auta Waziri

album: Na Taka Kaya (Album)


Yauwa
Auta Waziri kuke ji
Dan Majen Gombe (yauwa)
Gwmnan Gombe (eh)
Dan Majen Gombe
Inuwa Yahyan yan Gombe (gaske)
Gwamnan yanzu (uhm)
Kuma gwamnan mu na gobe
Lafiya Inuwa Yahya Dan Maje
Zaki sai dai zaki (yauwa)
Kura sai dai kura
Wani aikin sai gwamnati
Dan Maje na farko
Inuwa Yahya ku duba
Shi yayai karko
Sarauta kumah ga gwamna
Tun daga fari nasara shike ishe sa'a
Ku fada ku dada ga Inuwa Yahya Dan Majen Gombe
Ina Gombawa?
Ga Dan Majen Gombe na farko
Har tai haske
Dan gwamnan Gomben mu ta dauko
Gwamna kumah Dan Maje
Ina Gombawa? (Haya kai!)
Ga Dan Majen Gombe na farko
Har tai haske
Dan gwamnan Gomben mu ta dauko
Ku buga mini tambura da sunan Allah wahidi sarki
Wanda shi yayo bawa shi yaso kumah har yayo sarki
Sanan shi yayo Dan Maje muce masa hakimin sarki
Darajar manzonmu dan Aminatu gatane agun kowa
Rabbi ba don mu ba don su ba kare dan maje (Ameen)
Ga saraki giwa ga gwamna hakimi san kowa
Sai na tashi rannan da safiya sai na riski sakon Maina
Kai kuce alhaji Aminu Yuguda nan mutan amfana
General accountant na Gombe wanan da gwamna kwai fah amana
Kunji yarda yaran amshi
Tamburan sukai ba bashi
Maina shi ya kawo toshi
Shi yace mu dauko tambura
Muyi kida na Dan Maje gwamna
Ina Gombawa?
Ga Dan Majen Gombe na farko (haiy akai, eh)
Har tai haske
Dan gwamnan Gomben mu ta dauko
Kai, wane gwamna ne wanda yake da sarautun ban mamaki?
Wane gwamna ne wanda ya dau talakansa yake musu aiki?
Wane gwamna ne wanda kasar nan dukka akai masa maki?
Muhammadu dan Ahmadu
Inuwa Yahya ki gudu
Dan Majen Gombe
Matawallen Kaltungo (yauwa)
Matawallen ilimin ina fada
A fada musu gwamnan Gombe
Katukan Funakayye nan
Sadaukin Akko kenan
Inuwa Yahya barden Tangon kenan
Kirman Waja nace gwamna
Madakin maidagiwa
Magayakin Kalmai
Barden Arewan Tangale gwamna Gombe na dauko
Zaki kai bana ka haure, tsarinka duk suka dauko
Dan Majen Gombe
Aikinka kesa mamaki gwamna ka dada karko
Dan Majen Gombe
Sauran jihohi naji sunce da irinka ma suka dauko
Ga gwamna hakimin sarki

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists