Ruhin jikina Ruhin jikina ♪ Ruhi-ruhi nina zabo dai-dai Ruhin jikina kaine a sahun farko Ruhi-ruhi nima na zabo dai-dai Ruhin jikina kece a sahun farko ♪ Dadin kallo, baya kai in ka bullo ka iya tafiya Mai daraja ga ka, ka wuce parlour zuciya sai dai kurya Mai irin sunan ka, shima yana shan kallo a idon duniya Zan tafiya, daukar fansar mai zagin ka sam karka biyo baya ♪ Nayi murna sosai, dadi kamar ya kashe ni na samo ta Kyautar hula ta zan baki, ungo ki rike ta kiyi fifita Na boye suna, zan bayyana kauna gun yar gata Yaro jaye, kauce, ni da ita akwai kauna tun asalin mu so ne ya biyo baya ♪ In kayi ajiya, ba mai taba ma sai kai da kayi ta Dadin tafiya, ka rike masoyin ka don rai ya faranta Bana da fada, ammah a kan ka sai nayi ko ka fahimta Duk zuciyar da bata so ta wahala ba'a kallon ta ma balle ayi bibiya ♪ Na nazartu, ah-ah Na ko fahimtu Da karatu, muke cinye rubutu Mai garma shi ka sare tuntu Ko bayan raina ki sa wa 'ya ta bintu So ba'a sha cikin ruwa, ruwa ha-ahh Balle ka sayi a kasuwa, suwa ha-ahh So na da girma kasar mu Dacen mata sai kasar Nigeria Ah-yeah sai kasar Nigeria Ruhi-ruhi Nima na zabo dai-dai Ruhin jikina Kece a sahun farko Kai ne a sahun farko