Wacce nake so, ita nake so nakai gida na Duk mai zugan kanta zana ce masa, "To ina kira ruwa na?" Wanda nake so, shi nake so yazam mijina Duk mai zugan kansa zana ce masa, "Nima ina ruwana?" Oh ooh, ta gidana La la, oh ooh, na gidana Tattabara kike gun rike mini alkawari In banda ke na yarda zan sa cikin lamari Kyawun halin kine ya cika ni da alfahari Kinyi daban a mata zance naji har a gari Ke kinka basu rata Ana ahubbi ki mai nagarta Dani dake miji da mata Dana guje ki nayi wauta Mu gudu tare, masoyina Mu tsira tare Kamshin turare naji yau sai cikin amare Duk mai fadamin in barka zancen sa zana share Mun rufe kyaure, sirrika namu muyo a tare Bani biyar in baka goma Muyi zama cikin salama Tarko na akai ya kama Muje gida ka gaida umma Nayarda da kai, na amince muyi zama na sunnah ♪ Ina da tambaya, kuma ina neman sani Wai ya kike taji kaina? Daure ki fada mini Don naji sonki nata baiwa ruhi razani Ko kema haka kika ji, in hakane ki kula dani Ganin ki ke sakan natsuwa Naji kamar ina kahuwa Kece dai bakya canzuwa Hakan kwarai yana faruwa Zancen ka ya sakani amo Nayi dakon da babu gamo Shi hakuri tushen sa damo Mai sani zai sha romo Kaji gaskiya bakina kiran ka ya saba Hannun daya saba kirga asara yau zai kirga riba Samun ka yafi a samu tsaba Kaine ka azani kar turba Ka kama hannuna zana bika mu tsallake har gaba Oya-oya oya ahaa haaa Oya-oya oya ahaa haaa