Sadiq Saleh's production ♪ Zuciya tai na'am da ke farko A ganmu a bar mu tare sai kallo Zuciya tai na'am da kai farko A ganmu a bar mu tare sai kallo ♪ (Gbosa) (Gbosa) (Gbosa) (Gbosa) (Gbosa) ♪ Ungo mukuli na zuciya ta da ke Komai in zanyi dolle ne sai da ke Dukkan ciwon da ke jiki ya wartsake Kece mai bani magani ba ya ke Mai daraja ma kamar ki ya zan tsallake Bani bidar ko da dai dake a mafarki Ki alkhari garai ni, na rike Alkwarin namu baiwa ya rike Gara na baka rayuwata fansa Kayi ta ko ina babu mabusa Kowace ya ta ganka dolle ta kyasa Dan hakan ban sake a kanka na kasa Kayi gini a zuciya yayi rassa In da ke mun kaikayi ka sosa Dukka bakinciki na rai ka rusawa Kazama garkuwa garai ni ma dafa Soyayya (Gbosa) (Gbosa) (Gbosa) Ko yaushe in na kalle ki Jiki ke shiga shauki Sarauniya cikin zuciya Dan hakan daina mamaki Komai zanyi domin ki Ni naso ziran kugiya Hasken ki yafi al kuki Kamshin ki yafi al miski Da kin fito a kan sunkuya Na doka tambari naki Rawa nake a domin ki Zan so ki dan rausaya Soyayya Tallafa mai sanka kar ka barni masoyi Na rikide sam a kanka bani da shayi Ran da ka ce ka guje ni zanyi bulayi Dan haka shaida ni nawa sanka nakeyi Dukka sahun lokacin da za ayi yaye Babu kamar kai garai ni kai naga yayi Zafin so wahalar da zuchi yakeyi Zani fison muyi zama na adana kauna ♪ (Gbosa) Zafin rai na Sirri na Abar so na Jigo na Muradi na Sashe na Alkhari na Ina san ki, kina so na Babu abinda ya kai mini kai Cikin duniya Zuciya tai na'am da ke farko A ganmu a bar mu tare sai kallo