Kishore Kumar Hits

Umar M Sharif - Ango Amarya lyrics

Artist: Umar M Sharif

album: World Rhapsody Vol, 24


Umurni na iyaye, yakamata mu bi
Ban yarje ba, ahhh
Akwai zabi na, wayyo
Ke kar ki kusanta dani
Abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala
Iyaye sun ka hada mu mu daidaita ni kuma na yarda
Rayuwar aure na da wuya ko da soyayyar ma
Bare ni da ban sa son ki a raina ba ya zata kasan ce
A raina na ji hadin nan yayi sam-sam ba a kwafsa ba
Da ni da kai mun dace kowa ya gan mu ba zai kushe ba
Mu je gida don mu fada ma su kuma matsala ba mu samu ba
Na san kana so na bar wasan nan bana son jin sa
Rayuwar aure na da wuya ko da soyayyar ma
Iyaye sun ka hadamu mu daidaita ni kuma na yarda
Kowacce zuciya tana da abokin tarayyar ta
Wacce ta bi tawa komai bama ta tunanin kan ta
Don haka nima toh zuciyar akwai zabin ta
A duniya kowa na da masoyi keko ba nine ba
Mai yasa kake kyamata dan uwa ban gane ba
Ga mu jinsi daya addini daya bamu saba ba
Sannan umurni na iyayen mu baza na so muki bi ba
Mu yarje mu yo aure mai tsafta ba mai muni ba
Rayuwar aure na da wuya ko da soyayyar ma
Iyaye sun ka hadamu mu daidaita ni kuma na yarda
Koma menene za ki fadi nikam na yarda
Abinda Allah ya halatta a yi kika ce wahalula
Zuciya tawa da rudi ban rage ban gane ta na bada
Da sauran son ki a fannin yar uwa kar ki yarda na daina
Cikin sahun mata dole a sa da ni ba za a cire ba
Komai na yanmata kwai shi gare ni ko kai baka duba ba
Zama dani zaka ji dadi bazan bata maka rai ba
Ba zana yarje miki kara gaba ba za ki rasa ba

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists