Matan aure iyaye Kamannin mu da ke da idanu na gani So yabi jini farin ciki na kece Kamannin mu da kai da idanu na gani So yabi jini farin ciki na kaine Kece kinka zama farin cikin aure Ki zauna zuciyata in rufo kyaure Muyi wasa ba fada taho muyo tsere Ki daura ni a hanya kinji in nayi kure Nina yarda zama dakai koba jere Akwai babu na yarda haka zan jure Da dadi, da wuya hakan muna tare Mai son ya nufe mu da sharri Allah ya tsare ♪ Kece farko a cikin raina nayi ajewa Mata duka kin fisu guna baki da tamka Kaine farko a cikin raina nayi ajewa Zo kaban zoben zinare, ni in baka azurfa Ke kadaice gaki cikin rai babu wacce nake gani Rabin jikina inba kai ko a zahiri sam babu ni Ko'a runduna kece ta daban kinsha gaban su da kwarjini Cuta ta so da tayi mini kamu kai kayi mini magani Kin sha gaban su a kwarjini-kwarjini-kwarjini Kaine kayi mini magani ♪ Kece sarauniya Na baki zuciya Kece guda daya Duniya ta masoya Nice sarauniya Na baki zuciya Kaine guda daya Duniya ta masoya Sam babu shamaki waye zai min? Birki a son ki babu mai taka min Uwargida-amarya, ake ce min Kaine mijina ni kadai ba mai kwace min La-la-la ki daina fargaba Koda da yan daba Karyarsu su rabani ni da ke uwargida ♪ Bayan ke a zuci babu kowa Uwargida ta daga ke na rufe Bayan kai a zuci babu kowa Miji na aure mai sani farin ciki Ni ke nake gani ko cikin mafarki Duk wanda ya taba ki zani dau mataki In killace ki in saka cikin akurki In baki kula don kin zamo mata ta aure Na dace so Na more so Na samu a sauki Na shuka so Na girbe so Yau gani a daki