Fadli falala daga Allah ne, ke in kin samu Ki zamanto mai yin godewa, zai miki kari Fadli falala daga Allah ne, nina samu Na zamanto mai yin godewa, don yayi mmini kari ♪ Haduwa, rabuwa daga Allah ne soyayyah Shakuwa da uwa sanadi shine tarayya Hanuwa, samuwa sai wanda yaso ya shirya Jikuwa da ruwa watsa mini nina shirya Wakar ki nake yin rerawa Da kida na zo kiyi takawa, maza In naji kida naka tilas ne in taka Muryar ka idan naji sai nazo gaishe ka Burina bai wuce in zamto matar ka A gidan ka in girka maka tuwo da miyar kuka Addu'a kullum sai na roka Inga auren mu an daurawa, maza Fadli falala daga Allah ne, ke in kin samu Ki zamanto mai yin godewa, zai miki kari ♪ Fadli falala daga Allah ne, nina samu Na zamanto mai yin godewa, don yayi mmini kari Tafiyar ki a sannu ki taka kinji yar mulki Ko nawa a yanka zana biya sadakin ki Don kinyi daban bakya boyo kaman doki Za'a kirga dubu kafin a samu tamkar ki Na zo ki saka ni a fadar ki Na yarda cikin ta na zaunawa, maza Allah ya hada mu da kai kan so mun dace Banjin maganar kowa na zama kurma ce Na fidda guda a cikin su dubu na tace Kaine zakara na, dukka sa'a na zarce Na tabbata ni mai sa'a ce Dana same ka nayi morewa, maza Fadli falala daga Allah ne, ke in kin samu Ki zamanto mai yin godewa, zai miki kari Fadli falala daga Allah ne, nina samu Na zamanto mai yin godewa, don yayi mmini kari