Naka-naka ne don Allah kar ka juya baya Nice madubin dubawar ka karka bani kunya Naka-naka ne mai sona ya farin ciki na Nasan baka bani kunya garkuwan jiki na Naka-naka ne zancen nan ba karya kuke ba Nawa tuntuni na samu madubin dubawa Tshohuwar zuma ita ce magani inka sha ka warke Zani so kasan wannan lakani masoyi na da sake Bazan yi takara da yarinya ba masara da wake Ko fa haihuwa na fita, na taho ka duba ni Naka-naka ne mai sona ya farin ciki na Nasan baka bani kunya garkuwan jiki na So na gaskiya bai buya kowa na ganin shi Mutunci madara in ya zube dole ne a barshi Wanda yayi ma nisa sai dai da ido ka gan shi Wani hanin ga Allah baiwa ne nagode Allah na Naka-naka ne don Allah kar ka juya baya Nice madubin dubawar ka karka bani kunya Shi yabon kai jahici babu kyau ga kowa Jijji da kai da nuna isa baya dacewa Shi zai kai mutum ga halaka ba ruwan kowa Gaskiya guda daya mai kinta shi zai rasa hanya Naka-naka ne zancen nan ba karya kuke ba Nawa tuntuni na samu madubin dubawa ♪ Naka-naka ne mai sona ya farin ciki na Nasan baka bani kunya garkuwan jiki na Kece kika share hawaye na bazan manta dake ba Yanda ni nake ji yanzu bazan iya babu ke ba Kin zamo madubin dubawa ni ke zanyi duba Babu su gaba na yanmata ga hannu ki jani muje Naka-naka ne don Allah kar ka juya baya Nice madubin dubawar ka karka bani kunya Na rike da karfi soyayyar ka bazan saki ba Nasan nayi dace samun irin ka sai an duba Kai kawo da mata suyi su gama ni bazan gani ba Tunda na sani kai wanene ban tada hankali na ba Naka-naka ne zancen nan ba karya kuke ba Nawa tuntuni na samu madubin dubawa Bani son ka janyo min raini zani sanya duka Wanda ya taba mini mata ta lallai zaiyi kuka Mai kake nufi ko tafi ni ne? In sani a gun ka Kece zaki auna ki gani ki baiwa kanki amsa