Soyayya ce, nayo dace Da nayo kuka, yau ya kare Soyayya ce, nayo dace Masoyi bar kuka, ni zan share ♪ Komai yayi mafari zaiyo karshe Komai yayi tsauri zaya gushe Wanda yake da jari zai sana'a ashe Wanda ya shuka hakuri riba zai kwashe Ni na jaraba Yanzu ku duba Ni naci riba Kunci ya kare ♪ Mai imani dole za'a jaraba shi Har kan sa ya kulle ya kasa bude shi In yayi hakuri a sannu zai ga sakamakon shi Misali gani nan zan maye maka gurin shi Zan sa kayi murna Kar kayi kuna Da kai zan zauna Hawaye in share ♪ Gani a duniya sabuwa rayuwa ta canza Bani da damuwa ke kika zo kika min visa Godiya da yawa baki na gare ki ya furza Kyakkyawar masoyiya zuciya ke bata canza Na daura baza Rawa nayi girgiza Ina yin shi da izza Haushi na cire ♪ Dani da kai zamu zam abin kwatance Mata da miji haka babbar nasara ce Idan da shaidu ayi komai a mutunce Duk wanda bai so ya gani ransa ya bace Mu mun dace Da soyayyah ce Mai riba ce Karshen ta da aure Soyayya ce, nayo dace Da nayo kuka, yau ya kare ♪ Soyayya ce, nayo dace Masoyi bar kuka, ni zan share Soyayya ce, nayo dace Da nayo kuka, yau ya kare