Ungo zuciyata Kije ki adana ta Nasan zakiyi mata gata Ba wanda zai tabe ta Ke nafi so da soyayya, soyayya Ban da kamar ki a duniya, duniya Yabon ki nake na daga murya, daga murya Ki kusanto karda ki ja baya, ja baya Tauraruwa Ni kika haskawa Nayi mantawa Damuwa ke kika sawa Nema kansa samuwa Godiya na kawo daduwa Ni da ke bama rabuwa Mun zama tamkar d'a da uwa Alkawari ka rike Komai wuya, kar mu rabu ka ji Alkawari ki rike Komai wuya, kar mu rabu kin ji Kar mu rabu ka ji ♪ In ka kira ni gani Ga hannuna jani Karda ka yada ni Kai na tsayar gwani Mun shaku mun sabu Inda rai rabu Aure za muyi dibu Ba taba Zan share maka hawaye In dau huduba ta iyaye In kauda zuga ta kawaye Na haye, ye, ye A zuciya banda kamar ka Komai nawa ya zama naka Na jidadi da kyautar ka Ranan ka siyo mini sarka Alkawari ki rike Komai wuya, kar mu rabu kin ji Alkawari ka rike Komai wuya, kar mu rabu ka ji