Zahra-Zahra-Zahra Zahra-Zahra-Zahra Kece tauraruwa Zahra (Zahra) Kyakkyawa, kina da kyau na sura (sura) Cikin ruwa ni na tsinci allura (allura) Da zanga kamar ki da zana kara (kara) Na zam mai sa'a, nayi fara'a, na zama zabin ki Diya da dabi'ar kyau ga da'a nine angon ki Zahra-Zahra-Zahra Kaine likitan zuciya dake duba ta Mai jinyar ta a sa'ilin ta kamu da cuta Yau ta warke ba abinda ke damun ta Ka canza mata yanayin ta ka sabunta Na dau alkawar zuciyar ka zana faranta Abinda kayi min kudi basa iya biyan ta Zahra-Zahra-Zahra Zahra Ta yaya zan iya fassara kalmar so da baki Koko inyi misalin yanda ake ji a jiki Ido baya iya gani So kan iya saka tunani Mai kyawu koko muni Nidai in kun kalle ni Alamu sun nuna ina jin shauki Ina tare da Zahra babu jin raki Zahra-Zahra-Zahra Ajiyar so daka min ban rike wasa ba Ko dillali yazo bazai mini wayau ba Harda aku bazai bige ni da zance ba Duk su taho su tadda kai ban ji tsoro ba Ka zama ginshi ki A ido ko haki Nayo farmaki in cafke masoyi Zahra-Zahra-Zahra Zahra Zahra-Zahra-Zahra Zahra-Zahra-Zahra Zahra