Kuzo mu taka mata Kuzo mu taka mata Kuzo mu taka mata Kuzo mu taka mata A yau mu nuna bajinta M Shareef na dau gangata zana doka A yau farin cikine yasaka zana taka Aure akayai na 'ya'yan gata babu shakka Kowa yanata sa albarka Shareef Umar inayin waka Ku marmatso tayani mu taka Ranar kuke jira yau tazo Dangi maza da mata sun zo Abinci babu mai cin kanzo Baban biki na ango gwarzo Halin shi yanzu ni zan barzo Angonki Nura M Inuwa ♪ Angonki Nura M Inuwa Kinyo dace dashi garkuwa Lemarki zaya kare ruwa Gareki zaya zam inuwa Nasan halin sa badamuwa Yana da hakuri mai yawwa To rike shi kar kuyo rabuwa Komai da lokaci zahiri Aurenku anyi ayiriri Muna biki muna bidiri Saura ku haifi dan jinjiri Muzo suna miyo ayari Ga Nura yazamo nakine An daura yanzun mijinki ne Ke amarya shi ko angonki ne Gidan shi zaya sauke ki ne Ki zam uwa ta 'ya'yan shi ne Kinada hankali an fada Ni nasan zaki gyare gida Ki mai miya kisa man gyada Ya dinga santi har yayai tsida Hadinku yayi kyau na fada Ba'a abinda zanace ma kayi Kai kake fada ma wasu har suyi Shawarin zamo idan zasuyi Kare hakki nasani zakayi Nura nasan kanada tausayi Zamanku lafiya shine nata Mutu ka raba shine manufata Sharri-sharri Allah ya tsare ta Allah ya amsa addu'a ta ♪ Ga Nura ga Amina Allah yabar kauna Kun dace da juna Wayyo ni raina Yau na gwada murna Aurenku na kauna Na doka kidana Na rero wakana Auren Nura-aa-ah Amina ce amarya Amina, Amina, Amina Allah ya bada zaman lafiya