Mansoor-Mansoor Mansoor-Mansoor Jirgin soyayya Mun hau mun lula, hahaa Jirgin so za ya tashi ke daya ake jira Yar gata duniyar so kece da sarauta Jirgin so za ya tashi ka daya ake jira Dan gata duniyar so kaine da sarauta Mansoor-Mansoor Mansoor-Mansoor Na dawo gun ki nazo bako da sallama Kai kawo nayi karshe a kauna na tsunduma Kin jawo nayi roko nazo ki ban zuma Na sawo daga tufa ta mai kyau da karrama Ke nayi wa kwalliya ta shiga ta alfarma Nayi rawa inkiyata sunan ki a sama Mansoor-Mansoor Mansoor-Mansoor Na tarbo ungo kauna rike ka adana Babu dabo ka tsaya chak a zuci ka shina Kai sabo kuma tsoho hakan kake a raina Babu kobo na amince gidan ka in zauna Nayi nisa bani jin ku, kubar ma kira na Sai naje gun masoyi rike ni da sallama Mansoor-Mansoor Mansoor-Mansoor Soyayyah gaskiya ce ya zanyi in raina Wanda yake a cikin ta nima don na zauna Tarbiyya ko'a karshe ashe a kan gane mai ita Zantukan ka dukan su sun nuna Nayi dare ban masauki gidan ki in kwana Zo ka shige har abinci, zan maka kwadon rama Mansoor-Mansoor Mansoor-Mansoor ♪ Rike sirri sai mai sirri Ahhh ahhh Kinta fari a cikin taurari Ohh hoo Mai hakuri shi ke kan tsari Ahhh ahhh Ka zamo nagari ba'a yi maka gori Ohh hoo Nayi nazari tun a fari kece na saka buri Ya ta gari, zo da kaina bani hanun ki in kama ♪ Kaina fitar da kai nake son mu rayu Naga kana da tausayi gun marayu Zanen dutse hali ance baya boyu Na rabo jikin ka ko zana boyu Ga wanka, kwalliya kai na kira da dan gayu Nayi sa'a da masoyi ban yin nadama Mansoor-Mansoor Mansoor-Mansoor