Ayyeah Amana ki bani inda yarda Soyayya a kan hakan take yin karko Amana ka bani inda yarda Soyayya a kan hakan take yin karko ♪ Dadin bacci ke saka ayo minshari Ita wuya ko sai tasa ayo kakari A kallo ko a gane yanda nake a tsari Alamu sun nuna babu sauran buri Indai zanyi rayuwa dake Masoya cikin su za na zama na farko ♪ Tukwuici na so ka bani kauna yafi In boye a zuciya na sa mai murfi Cikin raina ka riga da kayo karfi Ka kai matsayin da baka yi mini laifi Amanar da ka bani na rike Idan ka kira ni ba jira zan sheko ♪ Kina kyau da kallo, idanun gani na Idan kinka bullo, sun koma Tufa yafi yalo, abin marmari na Sai nayi musu gwalo, in rama Kina nan ba abinda zana nema A fanin so ba abinda zai mini tsaiko Amana ka bani inda yarda Soyayya a kan hakan take yin karko ♪ Amana ki bani inda yarda Soyayya a kan hakan take yin karko Dacewa cikin so, nina fi kowa Masoyin dana so na kama Duk inda ya doso, yakan burge kowa Baya yimini kwafso haka nima Na zabe ka bani babu rama Faranta maka rai zan dada in ninko ♪ Amaryata zani baki suna Mijina ango idan da kwana Za nayi murna inga wanga rana Za nayi kuka daga cikin idona Kukan dadi ne abin nufi na Nima zanyi hakan dani dake muyi anko ♪ Amana ki bani inda yarda Soyayya a kan hakan take yin karko Soyayya a kan hakan take yin karko