Kishore Kumar Hits

Hausa Soundtrack - Shagwaba Tk Adam lyrics

Artist: Hausa Soundtrack

album: Shagwaba Tk Adam


'Yan mata mai ya faru?
Mai ya faru?
Yau dai ba kiyi mini zance ba
Wanene ya taban ki?
Ki nunan shi idan bai ga fushi na ba
Ba kaine ba masoyi
Kaine yau baka kawon chocholate na ba
Kanwata kiyi hakuri
Rigimar ki kamar ba'a gama raino ba
Ni sai ka goya ni, a kafadar ka
Ko kuma kayi mini bambu, ko kuma inki shiru
Dukka abinda kike so, haka zanyi
Kauna bata zama laifi ba
Nayi dace da masoyi, dan yayi
Guna bai gaza raino ba
Nine daya na biya ki, kuma na iya ki
Rikon ki bazai zama kowa ba, yanmata na
Musha kauna yarinya, musha kauna
Musha kauna duniya labari ce
Musha kauna dan yaro, musha kauna
Musha kauna duniya labari ce

Na zama sirikar umma, sirikar baba
Su suka haifa min miji mai gyara zaman duniya
Na zama sirikin baba, sirikin mama
Su suka haifo min baby mai saita zaman lafiya

Duk inda kaje Rabbana ya kare ka
Ka dawo mini lafiya ka zo mu kasance
Bana so mata su kalli fuskar ka
Duk wacca ta kalle ka Allah sa ta makance
Ko sun kallen ma ba zana gane ba
Duk inda naje son ki ne yake bina
Kuma duk inda naje ji nake kina ji na
Ko wata na gani ke kike gizo a bisa idaniya

So mai son ka, ka more soyayyah
So mai son ki, ki gane soyayyah
Son mai son wani yana ban tsoro ne
Ni dai na sani son maso wani cuta ne
Ni dai na sani masoyi dadi ne
Nima na sani masoyi dadi ne
Ni dai ga tawa nan da nake riritawa
Ke nake fifitawa
Kinfi kowa tawa
Yar dimurmur tawa
Yar dimurmur tawa
Dimurmur
Yar dimurma tawa

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists