Ga amsar tambaya Ga amsar tambaya Zana sanar miki amsar tambaya A cikin zuci babu kowa sai ke daya Zana sanar maka amsar tambaya A cikin zuci babu kowa sai kai daya ♪ Farashin sanki a garan yana kara tashi Ba rana ta faduwa Na zaga ko ina na duba ba kamar shi In ganci a kasuwa Yau gani cikin aji na sanki bani fashi Koh lati wajen zuwa Na dau darusa Kowa zan kasa In hau can bisa In musu kallon daya daya ♪ In nayo farin ciki kai kasa In nayo bakin ciki bayka kusa Indai gaka ba abunda zan rasa Da fitowar ka dole sai kowa ya gusa Kauna ka dasa Karda ka kwankasa Tini na bar masa mukullai baki daya ♪ Dawisu fito su ganki karshen kwalliya Taka sannu abinki sarauniya Indai ina nan gareki zinariya Kowa na so ya gan ki duk duniya Salo gun tafiya yan mata suzo gareki Nan ne zasu kwaikawaiya Komai kin iya Shinkafa da miya Farfesu nan gurin kikai zara gaba daya ♪ Nice taka da ka kira baby ban canja suna ba Na dau alkawar kuma zana cika bazana jefar ba Minjina ince maka ko ina bazan ji nauyi ba Har yau gobe in dai zaka tsaya bazan ga kowa ba Samarin zamani Sun zozo mini Ba wanda yayai mini sai kai daya kwali daya ♪ Ah-hh-hh-hh-hh-ah Ohh-hh-hh-hh-ah