Juya, kalli rawar da nake kyakkyawa ce ke Kauna zan baki Juya, kalli rawar da nake kyakkyawa ne kai Komai zan baka ♪ Daga ke ba sake anyi angama Na mallake komai babu haddama Na rayu da kauna kinga na jima Kar kiyo nisa babu sallama Gyara, kunnai ki saurara Lura, ba mai cika gurbin ki ♪ Ra'ayin ka fada mini in na fahimta Biyayya zan maka Zumar san ka ka sammani, bani na sha Tana sa ka warraka Ku ja da baya ku bar mini, mata Ni dai za a daga Sannu tirmi sha daka, jani ka kai ni inda ka so ni zan bi ka ♪ Da aminci yarda zamu shige daki Kai mai zagin masoya Hasada take Sai na killachai wadda nake shawqi Kin iya taku shiyasa na biyo ki Karshen hadewa ke ake nunawa tawa Gwanatar ke domin ki ♪ Labullai sirrin mai daki Rufa ni ka saya ni Ana damun mamaki su ke birge ni Ko an aje ni gidan ka karda su kallai ni Zo ka zamu hijabi karda su lashai ni Ba wasa, kamar ka ba irinsa busa sarewa na birge ni ♪ Juya, kalli rawar da nake kyakkyawa ce ke Kauna zan baki Juya, kalli rawar da nake kyakkyawa ne kai Komai zan baka