Ance min so ruwan ne Cikin zuciyar yayi zaune Sanki a zuciya, wajibi ne Cikin jikina don ruhi ne Na fada miki, kin bin jinin jikina, kawai kibar ni na rayu dake Mai san ganin murmushina, kar yayi min zance babu ke Bani zama wajen da ba ki, tillas sai na tsallake Nai imani da sanki zana mace, har zuwa goma ta karshe Ba'a dole a soyayya a mana tunda nace sai kai Sai na kai goma ta ƙarshen Da burin in kwashi adashin Domin na biya duka bashin Kyautatawar da kayi min Tunda da sanka ni na fara, ba batun in yada shi Wanda yaso yayi min dabara kasani zan kau dashi Ya bi jini yabi tsoka, sanka yabi har ma kashi Nai anniya a sonka zan jure, har zuwa goma ta karshe Har zuwa goma ta ƙarshe Ban mai gobe zata haifa ba Nai aniya bazan barki ba Ban san me zaki nema ba Harma nace bazan baki ba Komai kace zana ammince Kamar ni daya na dace Kamar ido zasu makance Zuciya ko ta dimauce Aljanna ta kike Wata ke kuma zara ce Idan har na mace Du'a'i kiyi min har zuwa goma ta ƙarshe Ba'a dole a soyayya a mana tunda nace sai kai