Zuci bata da zabi Ba batun lissafi Jiki babu karfi, soyayya che sila Mai yin so kabar yin haufi Aikin so kama da na tsafi So rijiya mai zurfi Mai sa canza kala A kan ki komai zana yi Karda fuska tayi mini sauyi Dama kiyi mini uzuri Zama dake nai ra'ayi Tausa zuciya ta zaki yi Domin tabar kada tambari ♪ Ido na ganin giftawar ki Kunne na sauraren ki Sa'in da nagga idanun ki Na gasgata ki Rayuwa mai kyau kin saita ni Tunda bakya so wata ma ta kulla ni Ki ja ni hani na ki a jiye ni Ki sanya kunne naki ki saurarai ni Kin shige zuciya Ina sonki gaskiya Matan da ke duniya Kin fi su iya soyayya Na zo mu dan zagaye Dake mu dan rausaya Kina bani kariya Babu mai jayayya Mu amfani lokaci Ina baki tabbaci Idan kinyi furuci Babu mai jayayya ♪ Zuci bata da zabi Ba batun lissafi Jiki babu karfi, soyayya che sila Mai yin so kabar yin haufi Aikin so kama da na tsafi So rijiya mai zurfi Mai sa canza kala ♪ Yan mata kyakkyawa Mai kyaun hali son kowa Ban yi miki yawa Ko na yi maki tsawa In babu ke soyayya Za'a ganni mashaya Bana yi miki karya Ki bani goyon baya (Na-na-na-na na-na-na-na-na)