Rana tunda gata ta bullo, zamu zaga duniya Gari a ko ina akwai haske, mun wayi safiya Muyai yadda aka saba, ba gudun dawainiya Mu rufe kar mu tona, sakon zuciya In ka samu ka gode In ka rasa ko ga gode Allah nace na gode In na rasa ma na gode In kasa wani dariya, dole zakayi dariya Kai dai rike gaskiya, allah ka rike daya Kai dai kabi gaskiya Komai tayi ta biya Rausaya muyi dariya Mu gode allah daya Da gaisuwa matan gida, amarya da uwar gida Zama kuyo shi da gaskiya, kuma dan allah daya Yace masoyiya Ta sace zuciya Zo maza yan mata zinariya Kemah sai ki tausaya In ka rayu duniya Gida mata da dukiya Makotanka ka tausaya Suyo bacci da dariya Ba mai baka banda alla Wani fata nei lafiya Wani na hanyar tafiya Wani yau ya shigota duniya Wani yau zai barta duniya Muyi du'a'i tun safiya Har zuwa lokacin kwanciya Ba mai baka banda allah Koh a tallo, idan ta kama dole in kwana Wanke allo, idan ka biya kaga ta kai ma Qolo, bacci yake ko babu taburma Kallo, ba mai yima in rabbi bai ma ba