So maruru ne So wani sirri ne Na kasa gane yaya kallar so take ne So mai sa hauka Ka manta tsarin ka In har ka shiga taskar so Jiki dukka zai mutu ne ♪ Ga wasika nayi garai ki nayo Farincikin rai na ♪ Mai hana barchi Ba a gyan gyadi Mai kama duk jiki Ayi ta tangadi Baza na boye ba Dolle in fadi Dani da ke zan so mu zama mahadi Tun faduwar rana zuwa al fijir Sakon da ke zuciya shi zan isar Kin jaddada kuma na tabbatar Banga dalilin da zana bar farinciki na ba ♪ Farincikin rai na ♪ Ma sha Allah Alhamdulilah So shi ne ke sa zuchi ta rasa idon duba Ni ban saba ba Bazan jurai ba Dadin so shi ne nasani Ban san sharrin ba Rana da wata Zafi da sanyi Baza na juya ba Zuciya na suka Rai kamar zai fita Dan bamu gana ba So ne domin Allah Karki sa nai kwalla Ki kamar baki duba ba Sako na zuciya Ki kalli fuska ta So yana raina ♪ Ga wasika nayi garai ki nayo Farincikin rai na Gaki bani kulawa Zo ki daiban kewa Kyawun ki nayi yabawa Zo ki daiban kewa Wasika nayo garai ki nayo Farincikin rai na