Kishore Kumar Hits

Umar MB - Cikin Jinina lyrics

Artist: Umar MB

album: Cikin Jinina


Cikin jinina so yake
Kar ku raba mu kar ku sake

A cikin soyayya ni nasan sai anyi hakuri
So da akwai dachi zakin sa kau yafi sikari
Rana da wata akwai haske
Ni bana ganin wata sai ke
Ni tawa madarar yan mata kece
Lamarin so bazan miki karya ba
Ni ba gida ba, ba mota ba
Sai tarin soyayya
Kar ki wuce

Kar a tambayeni rayuwa ta da taki
Wacce zana zaba nai batu a bayyanai
Zan ce tawa ce zaki tafi daga nan ki barni nai
Kin manta da cewa rayuwa ta taki ce
Kalma ta bankwana bata da dadin fade a baki
Kai ni inda zaki kai ni yan mata ki aje ni a zuciya

Ina san furuchin ki
Dadin lafazin ki
Motsin gabban ki
Su ke saka ni shawki
Zanchen nan da nayi kunnuwa baza su gane ba
Furuchin da nayi baza a boye wa ruhi ba
Kece linzamin zuciya
In na barki, kau zan sha wuya
Rabuwa dake ba lafiya
Cikon jin dadin duniya

Soyayya ta kama ni

La-la-la-la
La-la-la-la
La-la-la-la
La-la-la-la

Cikin jinina so yake
Kar ku raba mu karko suke

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists