Madubi ke nayi dubawa saurari bayani na Soyayya linzami na karbe ta ki jani Assalam-salam, Assalam-salam Assalam-salam hmmmhmm ♪ Nayi sallama sam baki amsa ba, saurare ni Da baituka na taho domin ke, sabon launi A zuciyata kin yi caraf soyayyar ki ta kama ni Ki yarda da soyayya ta, agaza in samu sukuni Farin ciki na, kuma burina kaunar ki ki bani Gare ni yau kin zama yar lele sha zaman ki ki huta ♪ Zani so ka bude kunnin ka da hanzari saurara Dube ni babbar mace ce mai jan aji dan lura Tako na daban yake ko a cikin mata nayi zarra Zancen in baka gane ba, gaba mayi bayani ♪ Dabi'un ki kaf dana duba yanmata su suka jani Jan aji, yanga, kyakkyawa, samsam baki da muni In same ki matsayin matar aure ba sauran raini Dani dake ko bamu dace ba? Duba fah ki ganni Dani dake ko bamu dace ba? Duba fah ki ganni ♪ Cikin mazaje ba kowa ne ba zan yarda in so shi Sai wanda ya amsa sunan sa namiji kauna zan ba shi Lallai kayo sa'a tunda na yarda na sauke farashi Dani da kai tabbas na yarda za muyi soyayya Na yarda zo muyi soyayya ♪ Nayi farin ciki Ba sauran bakin ciki Godiya zan miki Don kin bani mulki Lallai za'a sha biki Ango zan zamo miki Eh bikin mu za'ayi babban taro, auren soyayya Ko basa so auren soyayya ♪ Assalam-salam, Assalam-salam Assalam-salam hmmmhmm Wa'alaikas salam, nina amsa maka Wa'alaikas salam na amsa masoyi na Assalam-salam, Assalam-salam Assalam-salam hmmmhmm (Assalam-salam hmmmmhmm) (Assalam-salam hmmmmhmm)