Kishore Kumar Hits

Umar M. Shariff - Yayan Baba lyrics

Artist: Umar M. Shariff

album: Madubi


Hubbi-ii-ii-ii-ah
Hubbi

La-la, hubbin so zahiri
Har yau ban samo wace zan so ba
Baban yaro nake
Yan mata kowace ni take duba

Wani in zai furci
Zai fadi abinda yake mai dadi
Karya bata wuya nagane hakan ku fahimci zancena

Eh zan fido furci sarari sako ne zan cikin hikima
Kamala shike sa a taro bako cikin girma
Auta na maza nake, mata kowace ni take nema
Wata na jiji da kai
Dama ki bari matsayinki bai kai ba

Mai yi baya fada
Sai dai kaga har ya aikata sarari
Mata ko daban-daban ne
Ko wace da ajin ta ba fari
Wata na ajin farko
Wata ko ta zarce wa yan kore
Ni ba sai na fada ba
Amsar na gare ku yan kallo

Kowa yayi zagi a kasuwa
Yasan wanda yake na gano
Wanda ya tabo ni ya taba zafi
Wai borkono
Ni na wuce tsararki
Dukan manufofinki na gano
Ni bazan so ki ba
In zan aure sai na zabi kyakkyawa
(Sai na zabi kyakkyawa)

La-la, hubbin so zahiri
Har yau ban samo wace zan so ba
Baban yaro nake
Yan mata kowace ni take duba
Zancen da kake fadi
Daga ji kowa yasan kai karya
Kyawun 'ya mace
Nice kat daga kaina ai baya
Nice mace mai aji ga ido
Gashina har gadon baya
Makaranta nai fice
Har cikin gari na zama sha kallo
(Sha kallo)

Kowace shine ma, shine ma
Kema kin fadi a baya
Maza chanza madubi
Dan na gidan ku tabbas yayiyo karya
A cikin kyawawa babu ke
Abokai ko nayi karya?
Basa fadi gaskiya ba
Nasan dole su goya ma baya
Hubbin so zahiri
Har yau ban samo wace zan so ba
Baban yaro nake
Yan mata kowace ni take duba
Ni tunda nake 'da namiji bai taba furtan wanga zance ba
Watakila kawaici sukeyi miki kinga ni ko bazan yo ba
Kaima kyawun ne da kai?
Na dubaka tatas ban gano ba
A hakan kika gani kinka kyasa
Zancen ki bazana karba ba
Wani in zai furci
Zai fadi abinda yake mai dadi
Karya bata wuya nagane hakan ku fahimci zancena
Hubbin so zahiri
Har yau ban samo wace zan so ba
Baban yaro nake
Yan mata kowace ni take duba

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists