Bazan barki ba Lala nima bazan barka ba ♪ Na rike ki bazan barki ba Zani so mu zauna a rayuwa Ke na bai wa sirrin zuciya Ki rike ni amana kin jiya? Na rike ka bazan barka ba Zani so mu zauna a rayuwa Kai na bai wa sirrin zuciya Ka rike ni amana ka jiya? Zuciya jiki na, naki ne Ke na bai wa komai kin sani Kin zamo ni, na zama ke tuntuni Ba abinda ya rage ko kankani Duka sirrin dake a cikin zuciyata Na tattaro gare ki zan zayyana Duka sirrin dake a cikin zuciyata Na tattaro gare ka zan zayyana Na rike ki bazan barki ba Zani so mu zauna a rayuwa Haduwar da muka yo ni da kai Soyayyah muka kulla kan gaskiya Zuciyata tayi na'am rayuwata da kai zan zauna duniya Kan halayyar ka bani da fargaba Adali ne masoyi na kun jiya Kan halayyar ki bani da fargaba Zan zamo adali a gun ki sa a zuciya Na rike ka bazan barka ba Zani so mu zauna a rayuwa ♪ Na rike ki bazan barki ba Ka rike ni amana ka jiya Yayyafi ya sauka gari yayi sanyi Da bargo na son ki na rufe jiki na Rana daya in har ban gan ka ba sai nayi juyayi Na sanya ka a rai don Allah karka sani rana A cikin zuciyata kece mai yayi Abadan bani so ran ki yazam da kuna So gamo na jini ne babu karya A cikin su malami ne kai na samari ♪ Babban farin cikina a daura mana aure Mu zauna a daki dani dake a tare Ranar da zanyi ma kwalliya irin ta amare In zana lalle a jiki na in fesa turare Daga ranar na bar damuwa tunani ya kare Nazam mai gida gun ki lallai na more Son ki ya fitine ni, ya hana ni sukuni Shin ina zaki kai ni masoyiyata? Na rike ka bazan barka ba Zani so mu zauna a rayuwa Ke na bai wa sirrin zuciya Ki rike ni amana kin jiya?